Majalissar dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da hada wani abin fashewa a kasar.

A jiya Laraba ne majalissar ta dattawa ta amince da kudirin na daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da hada abin fashewa ba tare da zabin tara ba.

Majalissar ta amince da dokar bayan wani rahoto da aka bayyanar gabanta game da albarkatun kasa da kuma karafa.

Ta ce masu hada ababen fashewa suna yin amfani da kayyakin zamani domin kere-keren abin fashewa.

Sannan ta ce yawanci ababen fashewar da ake amfani da su an yi sune da wasu sinadari a kasar.

Bayan haka majalissar za ta yi mahawara a game da kudirin kafin daga bisani a mikawa shugaban kasa ya sanya hannu ya zama doka ga kasa.

Majalisar dattawan Najeriya ta ce yan kunar bakin wake suna amfani da ababen fashewa domin hallaka mutane a mafiya lokuta sannan sun hallaka mutane da dama da abin fashewa a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: