Wani matashi ya hallaka mahaifiyarsa lokacin da ya caka mata wuka a ciki bayan wani sabani da suka yi.

Lamarin ya faru ne a karshen kwalta unguwar Rimin kebe karamar hukumar Ungwaggo a jihar Kano.

Wani shaida ya bayyana cewa ya na tsaye a waje sai yaji karar hajiya Jummai ta na neman taimako bayan shiigarsa yaganta a cikin jini.

Ya ci gaba da cewa Dan nata mai suna Iro kwarangwal sun samu jayayya da ita bayan haka sai ya caka mata wuka.

Shaidan ya ce sun yi gaggawar kaita izuwa asibiti, sai dai likitoci sun bayyana rasuwarta saboda ta zubar da jini.

Sannan rundunar yan sandan jihar ta kano ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce ana ci gaba da bincike domin kamo sa ayi masa hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: