Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa ba za a kawo karshen yakin da ake yi nan kusa ba a kasar Sudan.

Babban jami’in a majalissar dinkin duniya Martin Griffiths shi ne ya bayyana haka bayan wata ziyara da ya kai kasar ta Sudan Port kusa da Tekun Maliya.
Martin ya ce yadda wutar gabar ke kara ruruwa a kasar Sudan ya nuna fadan ba zai yi sauki ba a nan kusa a kasar saboda zafin rikicin da ake yi da bangarori biyu.

Ya ce duk wata hanya an bi don rabawa alumma kayan jin kai amma abun ya ci tura a halin da ake ciki.

Martin ya ce ya kirawo dukkanin Janar-janar din da ake yaki tsakaninsu game yadda za a tattauna amma ba su nuna alamar tsagaitawa ba don a yi sulhu.
Ya ci gaba da cewa bayan waccen yarjejeniyar da aka yi a satin da ya gabata ta rushe sai an dai so sanya wata yarjejeniya amma dai abun ya ci tura.
Ko a makon da ya gaba sai da daya dagacin mayan hafsin sojin kasar da ake gwabza rikici da shi ya ce a shirye yake da a yi sulhu kada ayiwa kasar lahani.