Ministan wutar Lantarki na Najeriya Abubakar Aliyu ya bayyana cewa kudin wutar lantarki da ake karba a Najeriya ya fi na kowacce Kasa arha.

Ministan ya tabbatar da hakan ne a ranar Alhamis a burning tarayya Abuja a lokacin da yake jawabi a gaban kwamitin wuta na Majalisar Dattawa tare da shugabannin wasu bangarori na hukumomin wutar ta Lantarki.

Ministan ya ce in banda Najeiya babu inda ake shan wutar lantarki a duniya a arha,idan aka yi duba da yadda ake kashe kudade akan gas domin a samar da wutar.

Abubakar ya kara da cewa duk da kokarin da gwamnati ta ke yi na ganin wutar ta wadaci ‘yan Kasa ,amma wasu mutane da dama ciki harda wasu manyan ma’aikatun gwamnati ba sa son biyan kudin wutar.

A yayin jawabinsa Manajan daraktan hukumar rarraba hasken wutar lantarki ta Kasa TRCN Sulaiman Abdul’aziz ya bayyana cewa rashin Biyan kudin kudin wutar da wasu manyan ma’aikatun gwamnati ba sa yi ne hakan ya sanya aka dage bai’wa kamfanonin KAEDCO na Jihar Karina da KEDCO da ke Kano daga Ma’aikatar wuta ta Kasa a kwanakin baya.

Daraktan ya ce koda yake an mayar musu da wutar take wucin gadi dole ne ya kasance an biya kudaden ga hukumar rarraba wuta ta Kasa a cikin kwanaki 60 da aka ba su.

A bangaren shugaban kwamitin majalisar Dattawan bangaren wutar Sanata Gabriel Suswam da sauran mambobin kwamitin sun bayar da shawarar cewa Ma’aikatar Kudi ta Kasa ta dunga cirewa daga asusun Ma’aikatun da ba sa biyan kudin wutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: