Wata babbar kotu dake zaman ta a kasar Birtaniya ta yankewa sanata Ike Ekweramadu hukuncin daurin shekaru Goma a gidan yari tare da matarsa.

Alkalin kotun Mr.Johnson shi ne ya bayyana hukuncin a yau juma a yayin zaman kotun.
Mr Johnson ya ce ya kama sanatan Najeriya Ike Ekweramadu bisa laifin yunkurin cire sassan jikin mutum a Birtaniyar.

Sannan ya ce ya Yanke masa hukuncin shekaru Goma a gidan yari da kuma matarsa Beatrice shekaru shida bayan kama su da laifin a kasar.

Sannan akwai wani Karin mutum guda da aka kama wanda shi ne ya kawo wanda za a cirewa kodar ba bisa radin Kansa ba Mai suna Obita Obinna.
Idan ba a manta ba a watannin da suka gabata ne dai wani mai suna Obinna ya dauki wani matashi dan tireda da cewar zai kaishi kasar Birtaniya domin samarsa da aikin yi.
Sai dai bayan kai shi sai aka yi yunkurin cire sassan jikin sa wato koda a sanyawa yar gidan tsohon sanata Ekweramadu Sonia bisa rashin lafiya da take fama da ita.
Lokacin da likitan da zai yi aikin ya tambayi matashin ya ce, bai san zance Koda ba kuma shi an kawo shi kasar ne domin samarsa aikin yi.
Nan take Jami’an Birtaniya suka kama wadanda ake zargin da yunkurin cire sassan jikin matashin tare da guffanar da su a kotu.
Sannan ko a cikin makon da ya gabata sai da shugaban majalissar dattijan Najeriya ya aike da wasika kasar Birtaniya domin sassautawa Ike Ekweramadu da matarsa sakamakon gudumarwa da ya bai wa Najeriya.
A yau dai babbar kotun ta yanke hukuncin kan Ekweramadu mai shekaru 60 da matarsa mai shekaru 56 da kuma Obinna da 51 dukkansu yan Najeriya.