Wata Kotu da ke zamanta a Sabo yankin Yaba a Jihar Legas ta bayar da belin shugaban Kabilar Igbo mazaunin Ajawo a Jihar Fredrick Nwajagu.

An gurfanar da Shugaban Kabilar ne bisa barazanar da yayi na kawo ‘yan ta’addan IPOB cikin Jihar a lokacin da ake fira dashi a gidan Talabijin na Channels.
Kafin bayar da belinsa sai da kotun ta nemi da a gabatar mata da shedu wadanda su ka mallaki kadarorin da aka yi musu rijista tare da kawo takardun kotu.

Lauyan wanda ake kara ya nemi da Kotun tayi adalci a hukuncin tare da rokon kotun ta bayar da wanda ake zargin beli.

Alkalin ya kuma bayar da belin wanda ake zargi bayan karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa.
Bababn mai Shari’a a Kotun peter Nwaka shine ya bayar da belin tare da Biyan tarar naira miliyan daya da kuma shaidu guda hudu.