Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallaka Wasu jami’an ‘yan sanda uku a yankin Umunze da ke cikin karamar hukumar Orumba ta Kudu a Jihar Anambra.

 

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Alhamis a lokacin da ‘yan ta’addan su ka kai musu hari shingen bincike da ke kan titin na Umunze-Ihite.

 

Rahotanni sun bayyana cewa zuwan maharan shingen keda wuya suka budewa jami’an tsaron dake bakin aiki wuta wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan uku daga ciki.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Tochuckwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Ikenga ya bayyana cewa yawaitar hare-haren ‘yan bindiga na daya daga cikin abinda jami’an ‘yan sanda ke fuskanta a lokacin da su ke tsaka da gudanar da aikinsu.

 

Kakakin ya kara da cewa duk da yawaitar kai hare-haren hakan ba zai sanya jami’an nasu su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da binciko masu laifi.

 

Sannan yace tuni su ka aike da jami’an ‘yan sanda domin kamo wadanda su ka aikata kisan.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: