Zababben shugaban Kasar Najeriya Asiwaju Bola  Ahmad Tinubu ya bayyana cewa daga lokacin da ya hau kan karagar mulkin Najeriya bayan an rantsar dashi zai cika dukkanin alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zaben sa.

 

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a garin Port-Harcourt ta Jihar Rivers, a yayin kaddamar da ginin harabar Kotun Majistare wadda gwamnan Jihar Nyesom Wike ya gina.

 

A yayin kaddamarwar Bola Tinubu ya jinjinawa Wike bisa kokarin da yayi na gina harabar, inda yace hakan zai kawo karshen cin hanci a bangaren shari’a, sama da kula da alkalai da tabbatar da ganin Sun shiga cikin walwala.

 

Tinubu ya kara da cewa zai tabbatar da ganin yayi adalci a lokacin mulkin sa tare da ganin ya hada kan Al’ummar Najeriya.

 

Sannan Tinubu ya nemi hadin kan mutanen Jihar domin ganin ya cika dukkanin alkawuran da ya daukarwa Al’ummar Najeriya a lokacin yakin neman zaben sa.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: