Gwamnan Jihar Cross Rivers Farfesa Ben Ayade ya sanya dokar hana fita daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 6:00 a garuruwan Oyonum Ofaturo.

Mai bai’wa gwamnan shawara ta musamman kan kafafan sada zumunta Chiristian ita ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Juma’a.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa dokar da gwamnan ya sanya a garuruwan guda biyu da ke cikin karamar hukumar Obubura za ta fara aiki nan take.

Ben Ayade ya sanya dokar ne sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin mazaunan yankunan guda biyu.

Chiristian ta ce gwamnatin ta bai’wa jami’an tsaro umarnin su mamaye dukkan garuruwan tare da ganin mazauna yankunan sun bi dokar yadda ya kamata.

Gwamnan ya kuma koka kan yadda aka rasa rayuka da dukiyoyi a yankunan biyu bayan rikicin da ya barke a tsakanin su, tare da bayar da tabbatacin cewa za a hukunta wadanda su ke da hannu a cikin rikici.

Leave a Reply

%d bloggers like this: