Jam’iyya mai Mulki ta APC a Najeriya da sabon shugaban Kasar Bola Tinubu ka Iya daukar tsohon Ministan Neja Delta Godwill Akpabio a matsayin shugaban majalisar Dattawa ta Goma.

Jagororin jam’iyyar ta APC kuma sun sake nuna goyan bayansu ga dan majalisar wakilai Tajudden Abbas a matsayin kakakin majalisar Wakilai na Tarayya.


Jaridar Punch ta rawaito cewa wasu majiyoyi masu karfi da su ka halarci taron sirri da aka gudanar a ranar Juma’a a gidan zababban shugaban Kasar Bola Tinubu ne sun tabbatar da hakan.
Wata majiya ma daga majalisar tarayya ta bayyana cewa har kawo yanzu ba a cimma matsaya ba akan kujerun mataimakin shugaban majalisar dattawa ba da kuma mataimakin kakakin.
Hakan na nuni da cewa mai yuwuwa jam’iyyar ta APC da zaɓaɓɓen shugaban Kasar su bar kujerun mataimakan ga ‘yan takara domin ayi zabe har ta ka kai ga wani ya samu nasara.
Ta cikin wani sako da Jaridar ta Punch ta samu daga majiyoyin sun tabbatar da cewa zaɓaɓɓen shugaban Kasa da jam’iyyar ta APC sun yarje da cewa shugaban majalisar dattawa ya fito daga Kudu maso Kudu yayin da kakakin majalisar wakilai kuma ya fito daga arewa maso yamma.
Jam’iyyar ta daukin matakin ne a gurin taron da ta gudanar a Ranar Juma’a, domin raba mukamai zuwa shiyyoyin.