Kotun sauraron korafin zaɓen shugaban ƙasa ta sanya ranakun 9 da 10 ga watan Mayu domin sauraron korafin wasu jam’iyyu.

Kotun ta ce sanya ranar Talata domin sauraron korafin jam”iyyar PDP da jam’iyyar APM.

Sai dai an ɗage sauraron korafin jam”iyyar LP wanda Peter Obi ya mata takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2023.

Kotun za ta saurari korafin jam”iyyar LP a ranar Laraba.

Haka kuma a ranar Laraba kotun za ta saurari korafin jam”iyyar APP a ranar.

Sai dai kotun ta yi watsi da korafin jamiyyar AA da ta shigar gaban kotun don ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa.

Jam’iyyun da su ka shigar da korafinsu kan zaɓen na ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa tare da sukar nasarar lashe zaben da Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: