Aƙalla mutane tara aka yi garkuwa da su bayan wasu da ake zargi masu garkuwa ne sun yi wa fadar sarkin Kagarko ƙawanya.

Maharan sun kai harin fadar sarkin Kagarko a jihar Kaduna tare da yin awon gaba da ƴaƴa da jikokinsa Tara da kuma wasu mutane uku mazauna garin.
Wani mazaunin garin ya shaida cewar mutanen sun nufi adar sarkin ne kai tsaye bayan sun kai harin.

Daga cikin mutanen da aka sace har da ƙaramar matar sarkin.

Sai dai maatar ta kuɓuta daga bisani ta koma gidaa.
Haka kuma sun yi wa wani Audu Kwakulu rauni wanda a halin yanzu ya ke asibiti bisa kulawar likitoci.
Sai dai jami’an tsaro a jihar ba su ce komai a dangane da harin ba
An kai harin ne a daren Lahadin da ta gabata.