Hukumar Hisbah a jihar Kano ta koka kan yadda masu adaidaita sahu a jihar ke manna hotunan batsa ko wasu abubuwa da ke bata tarbiyyar al’umma wanda ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.

 

Kwamandan hukumar, Sheikh Harun Ibn Sina ne ya bayyana hakan ga ‘yan jaridu a ofishinsa, inda ya gargadi masu adaidaita sahun da su kaucewa duk wani abu da zai gurbata tarbiyya.

 

Hukumar Hisbah ta dade tana yaki da gurbacewar tarbiyya a jihar da wadanda suka sabawa koyarwar addinin Musulunci da kuma al’adun Hausawa don ganin an dakile barnar.

 

Rahotanni sun nuna cewa hukumar ta Hisbah na kokarin ganin ta gyara tarbiyyar matasa da ya yi katutu a cikin jihar, musamman masu yada bidiyon TikTok na batsa.

 

Shugaban Hizbar ya ce sun samu bayanai cewa masu adaidaita sahu suna aikata laifuka kamar guda 3 da suka sabawa tsarin Musulunci.

 

Na farko, suna kunna wakoki kuma su kure sautinsu da ke damun mutanen da ke gefe, na biyu suna manna hotunan batsa wanda bai dace ba ko dadin kallo, na uku suna shiga wadda ta sabawa al’adun Hausa da kuma tsarin addinin musulunci, bayan kuma daukan mata da suke a matsayin fasinjojin su.

Leave a Reply