A hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke ranar Talata ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin gwamnan jihar Osun.

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 403,371 inda ya kayar da gwamna Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 375,027.

 

Amma Oyetola da APC sun ki amincewa da sakamakon zaben inda suka nufi kotun.

 

An gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 16 ga Yuli, 2022.

 

A hukuncin da ta yanke a ranar 27 ga Janairu, 2023, kotun mai shari’a Tertse Kume ta soke nasarar Adeleke tare da bayyana Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: