Ana tsammanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas zasu halarci taron da ƙungiyar gwamnonin PDP ta shirya.

Gwamnan jihar Sakkwato kuma shugaban ƙungiyar, Aminu Tambuwal, ne mai karban baƙin da zasu halarci taron wanda aka tsara gudanarwa a Transcorp Hilton, Abuja ranar Alhamis.

Babban Darakta na kungiyar gwamnonin PDP, C.I.D Maduabum, ya ce masani kan tattalin arziki, Muda Yusuf, zai yi lakca a wurin taron.

Ana tsammanin baki ɗaya gwamnoni masu barin gado da zababbun gwamnonin da za’a rantsar ranar 29 ga watan Mayu, 2023, za su halarci taron.

Zababbun gwamnonin da ake sa ran ganinsu a wurin taron sun hada da Seyi

Makinde na jihar Oyo, Umo Bassey Eno na Akwa Ibom, Peter Ndubusi Mbah na Enugu, da Agbu Kefas na jihar Taraba.

Sauran sun haɗa da, Siminalayi Fubara na jihar Ribas, Sheriff Oborevwori na jihar Delta, Dauda Lawal na jihar Zamfara da kuma Caleb Mutfwang na jihar Filato.

Haka nan mambobin kwamitin gudanarwa (NWC), mambobin kwamitin zartaswa (NEC)da amintattun jam’iyyar PDP (BoT) zasu halarci taron a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: