Mutane bakwai sun mutu yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti, bayan sun sha wani shayi da ake zargin an haɗa shi da Zaƙami, a wajen wani taron ɗaurin aure a Kano.

Shaidun ganau sun ce lamarin ya shafi kusan mutum 50, inda har yanzu ba a san inda wasu daga ciki su ke ba.
Lamarin ya faru ne a Sheka cikin ƙaramar hukumar Kumbotso a birnin Kano.

Ɗaya daga cikin shaidun mai suna, Sanusi Yahaya, wanda yaya ne a wajen amaryar, ya

ce ana zargin an haɗa shayin ne da ƙwayoyi daban-daban bayan zaƙamin.
Ya bayyana cewa ya zama al’ada ga matasan yankin, musamman masu shaye-shaye su dafa shayi lokacin biki, inda su ke fakewa da hakan su sha ƙwayoyi.
Sun dafa shayin sannan su kan su ba su san ko ƙwayoyi nawa ba ne a ciki, wanda har ya kai ga wasu daga ciki sun fasa sha.
Amma wasu daga ciki sun nace sai sun sha shayin, inda su ke cewa ƙwaƙwalwar su za ta iya ɗaukewa.
Wani shaidar mai suna, Abdullahi Muhammad, ya ce ya zuwa ranar Talata, mutum 7 sun rasu.