Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa a Najeriya FRSC ta buƙaci a dinga amfani da shari’ar Muslunci wajen hukunta masu karya doka.

Shugaban hukumar a Najeriya reshen jihar Bauchi Abdullahi Yusuf ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da kamfanin dillancin labarai a Najeriya NAN.


Ganawar da aka yi yau Alhamis, shugaban ya ce iya dokar tuki da aka yi ba za ta wadatar ba, ya buƙaci karin dokoki na shariar musulunci domin hukunta masu karya doka.
Ya ce hakan zai ƙara sanyawa matuka ababen hawa su sake nutsuwa tare da tabbatar da jin dokokin tuki.
Sannu ana samun yadda wasu ke tukin ganganci wanda hakan ke haddasa haddura.
Ya ce amfani da shari’ar Muslunci ne kaɗai zai sanya mutane su hankalta tare da bin dokokin hanya da kuma tuki.
Sannan saka dokar shari’ar Muslunci zai rage munanan dabi’u da matuƙa ababen hawa ke aikatawa yayin tuki.
Gudun wuce Sa’a na daga cikin abinda ke damun hukumar wanda hakan ke haddasa haddura.
Ya ƙara da cewa akwai dokokin da babu su wajen hukunta masu laifi kuma sanya shari’ar Muslunci zai karawa hukumar kaimi tare da rage yawan masu aikata laifi a yayin tuki.