Hukumar jin dadin alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana cewa kamfanonin jiragen sama na Najeriya guda hudu sun bukaci da a kara kudin aikin hajjin bana.

 

Shugaban hukumar Zikirullah Hassan ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sun bukaci da a kara $250.

 

Zikirullah ya bayyana hakan ne a birnin tarayya Abuja a gurin horas da jami’an hukumar na Jihohi a ranar Asabar.

 

Shugaban ya ce kamfanonin da su ka nemi karin sun hada da kamfanin Azman Air Peace Max Air Aero Contractors.

 

Zikirullah ya kara da cewa kamfanonin sun nemi karin ne sakamakon rikicin da ake yi a Kasar Sudan wanda hakan zai sanya sai sun bi doguwar hanya kafin su isa kasar.

 

Hassan ya ce maniyyatan ba za su biya ko kwandala ba akan Karin da kamfanonin su ka nema.

 

Kazalika ya bayyana cewa hukumar na duba hanyoyin da za a bi domin dauke karin da kamfanonin su ka nema.

 

Zikirullah ya ce hukumar ta sanya ranar 25 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa kasar Saudiyya.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: