Wata Kotun Majistiri da ke zamanta a Jihar Ondo ta aike da wani basaraken Kauyen Ade cikin karamar hukumar Akure ta Arewa Oba Adewale Boboye gidan a jiya da gyaran hali sakamako rushe wani gini da yayi tare da lalata bishiyoyi da amfanin gona ba bisa ka’ida ba.

 

An gurfanar da basaraken a gaban Kotun ne akan tuhume-tuhume shida wadanda su ka kasance akan barna.

 

Jaridar Punch ta rawaito cewa Ginin da basaraken ya rushe ginin cocin Apostolic ce wadda ke da mazauni akan titin Ado Ekiti yankin Igoba Akure.

 

Mai shigar da kara a gaban Kotun Ajiboye Babatunde ya shaidawa Kotun cewa Basaraken ya hada baki da wasu mutane a Kotun wajen aikata laifin.

 

Babatunde ya kara da cewa Basaraken ya rushe katangar Kotun wadda darajarta ta kai Naira Miliyan Daya da kuma bishiyoyin dabino da amfanin gona wadda darajarsu ta kai naira miliyan Biyar tare da Allon cocin.

 

Bayan karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa Lauyan Basaraken ya musanta zarge-zargen da ake yi masa tare da rokon Kotun da ta sassauta wa Basaraken yayin yanke masa hukunci.

 

Da take yanke hukuncin Alkaliyar Kotun Bukola Ojo ta yanke masa hukuncin shekaru Goma a gidan gyaran hali bayan ta same shi da laifukan da ake tuhumar sa dashi.

 

Kotun ta kuma bayar da umarnin biyan diyar naira Miliyan Biyar ga mai shigar da kara sakamakon rushe katangar cocin da bishiyoyin Dabino da amfanin gona.

 

Mai Shari’ar ta bayyana cewa idan Basaraken ya biya diyar za a soke hukuncin turashi gidan gyaran hali.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: