Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana dalilin da ya sanya gwamnoni Arewa su ka zabi Bola Tinubu a matsayin shugaban Kasar Najeriya.

Masari ya shaida hakan ne a fadar Sarkin Daura Alhaji Umar Faruq a yayin ziyarar bankwana da ya kai masa a ranar Alhamis.


Gwamnan ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar APC sun marawa Tinubu baya ne domin girmama tsarin karba-karba na jam’iyya mai Mulki.
Masari ya ce rashin bin tsarin karba-karba na Wasu jam’iyyun ya sanya su ka fada cikin rikici wanda yaki ci yaki cinyewa.
Kazalika ya bayyana cewa akwai jam’iyyun da basu yadda da tsarin karba-karba, inda su ka bayyana cewa tsarin karba-karba za a yi kafin lokacin zaben shugaban kasa da aka gudanar.
Gwamnan ya kara da cewa Allah ne ya ceto jam’iyyar APC daga Kunyata harta kai ga ta samu nasara a zaben da aka gudanar.
Masari ya ce ya kamata su tsaya tsayin daka wajen ganin Sun cika dukkanin alkawurin da suka daukarwa Al’umma.