Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanya maganin Yara na Zinc Sulphate wanda ake sarrafa shi a Najeriya a cikin ingantattun magungunan da ta Aminta su.

Shugabar hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta Kasa NAFDC Farfesa Majisola Adeyeye ce ta bayyana hakan.


Majisola ta ce maganin wanda kamfanin Swiss Pharma SWIPHA yake sarrafawa shi ne na farko da ya samu sahalewa yankin Saharar Africa.
Shugabar ta kara da cewa bayan samun amincewar wucin-gadi domin kammala gwaje-gwaje tare da cika ka’idoji wajen sarrafa magunguna wanda hukumar ta Lafiya ta sanya.
Majisola ta bayyana cewa amincewar ta samu ne hadin gwiwa da hukumar ta NAFDAC da kamfanin wajen cika sharudda da ka’dojin da hukumar ta Lafiya ta shimfida a lokacin gwaje-gwajen.
Shugabar ta ce nasarar da kamfanin ya samu hakan zai karawa sauran kamfanonin magunguna da ke Najeriya kaimi wajen bunkasa su.
A yayin jawabin shugaban kamfanin na SWIPHA ya yabawa hukumar ta NAFDAC bisa jajircewar ta har ta kai ga an samu nasara, inda kuma yayi alkawarin Samar da magunguna masu inganci.