Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Imo Hon Chinedu Elelian na kauyen Umuarugo a mazabar Umueze ta II cikin karamar hukumar Ehime Mbaino a Jihar.

 

Jaridar Leadership ta rawaito cewa ‘yan bindiga wadanda ake kyautata zaton makiyaya ne sun yi garkuwa Hon Chinedu ne yayin da su ka biyo sahunsa har gidansa a cikin wasu motoci guda biyu, inda zuwan su ke da wuya su ka fara harbe-harbe domin razana mutanen yankin.

 

Wata majiya a yankin ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun kutsa kai gidan Chinedu tare da sanya shi a cikin motar su ka tafi dashi.

 

Majiyar ta bayyana cewa har kawo yanzu masu garkuwa ba su tuntubi iyalan shugaban Jam’iyyar ba.

 

Masu garkuwar sun yi garkuwa da Chinedu ne kwanaki kadan bayan da wasu ‘yan bindiga suka hallaka wani tsohon soji Tony Enoch.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan Henry Okoye ya bayyana cewa  kwamishinan ‘yan sandan Jihar Ahmad Barde ya bayar da umarnin kamo wadanda su ka aikata laifi

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: