Wasu ma’aikatan gwamnatin jihar Zamfara sun gudanar da Salloli na musamman, a masallacin idin Gusau, babban birnin jihar ranar Asabar.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ma’aikatan sun taru a masallacin idin ne da misalin ƙarfe 10 na safe, inda suka nemi Allah ya kawo mu su ɗauki kan kuɗaɗen albashinsu.


Ma’aikatan sun bayyana cewa, rabon da a ba su albashi tun watan Janairu, wanda hakan ya jefa su cikin halin ƙaƙanikayi.
Wani daga cikin ma’aikatan wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa da kyar su ke iya samun abun sanyawa a bakin salati.
Ya ce wannan Sallar da suka yi, sun yi ta ne domin neman taimako wajen Allah, ya sanya gwamnan jihar da duk wasu masu ruwa da tsaki, da su tausaya mu su, su ba su ƴan haƙƙoƙinsu.
Anyi koƙarin jin ta bakin gwamnatin jihar, kafin kammala haɗa wannan rahoton ya ci tura, domin layin wayar kwamishinan watsa labarai na jihar, Ibrahim Dosara, a rufe ya ke.