Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta bukaci mazauna Abuja da su gabatar da ƙorafinsu a gaban kotun sauraron ƙorafin zaɓe bisa ƙin amincewa wajen rantsar d zɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Mazauna Abuja sun buƙaci kotun ta dakatar da rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar wanda su ka ce ya gaza samun adadin kaso a Abuja ga duk wanda ya lashe kujerar shugaban ƙasa.
Mai shari’a Inyang Ekwo a yau Litinin ya umarci mazauna Abuja da su miƙa ƙorafinsu ga kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Mazauna Abuja sun kafa hujja da sashe na 134 (2) (b) na kundin tsarin mulkin ƙasa wanda ya ce wajibi ne shugaban ƙasar da aka zaɓa ya samu kaso 25 na masu zaɓensa a Abuja.

Ƙorafin da su ka shugar sun yi ne da nufin kotu ta da sauran masu ruwa da tsaki su dakatar da shirin rantsar da sabon shiugaban ƙasar Najeriya da mataimakinsa.
Sannan sun buƙaci kotun ta yiw atsi da sakamakon zaɓen d aka sanar har sai wanda aka zaɓa ya cika sharuɗan sashe na 123 (2)(b) na kudin tsarin mulkin ƙasar.
Sai dai bayan umarnin kotun na ganin mutanen sun shigar da ƙorafin kotun sauraron ƙarar zaɓen shugaban ƙasa, an ɗage ci gba da shari’ar har zuwa ranar 18 ga watan Mayun shekarar da mu ke ciki.