Aƙalla manoma aka hallaka waɗanda su ka haɗa da mata da ƙananan yara a jihar Nassrawa.

Al’amarin ya faru a ƙauyen Takalafiya da ke karamar hukumar Karu a jihar.

Wani shaidar gani da ido mai suna Moses ya ce maharan sun zagaye garin riƙe da makamai sannan su ka fara harbin iska a cikin dare.

Daga cikin mutanen da aka hallaka har da wani malamin addinin kirista a garin da kuma wasu mabiynsa.

An binne mutane 38 a ranar Asabar waɗanda ƴan ƙauyen Takalafiya ne a garin Gwanja dake ƙaramar hukumar Karu a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Dakta Emmanuel Akabe wanda ya jagorancin tawagar gwamnati zuwa wajen, ya yi Ala-wadai a kan lamarin.

Akabe ya nuna kaɗuwa a kan lamarin tare da alkawarta cewar gwamnati za ta tabbatar an gudanar da bincike a kan lamarin.

Akwai wasu yankuna da ke maƙobtaka da garin da ake kai musu hare-hare tare da jikkata mutane ko ma hallaka su.

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: