Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai hari karamar hukumar Mangu ta jihar Filato tare da hallaka mutane 29.

Yan bindiga da ake zargi sun hallaka mutane kimanin 29 a kauyuka biyu da suka kai wa hari a jiya Litinin.

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin da misalin karfe tara na dare a wasu kauyuka kamar Fungzai da Kubwat.

Wani shaidar gani da ido mai suna John Yakubu ya bayyana faruwar lamarin ga jaridar Punch

Ya ce wasu yan bindiga sun shiga yankin Fungzai da yawansu sannan suka fara harbin mutane, kuma kowa ya sa gudu kuma hallaka mutane 15 a garin tare da yan uwansa.

Sannan ya ci gaba da cewa bayan haka sun shiga kauyen Kubwat nan ma suka hallaka mutane jimilla 29.

Ya ci gaba da cewa wasu na ci gaba da karbar magani a asibiti bayan binne 29 a makabarta.

Sai dai bayan tuntubar kakakin yan sandan jihar Pilato domin bayyana hakikanin abun da yake faruwa, sai dai bai samu damar daga waya ba.

A nasa bangaren gwamanan jihar Filato ya mika sakon ta’aziyyarsa ga ahalin wadanda lamarin ya faru da su bayan tura tawaga yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: