Mai magana da yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu, ya ce hauhawar farashin kayayyaki matsala ce ta duniya baki ɗaya ba iya Najeriya ba.

A ranar Litinin ɗin nan ne hukumar ƙididdiga ta ƙasa wato NBS, ta fitar da rahoto wanda ke bayani akan ma’aunin farashin kayayyakin masarufi wato CPI.

CPI na auna hawa da saukar farashin kayayyakin da ake amfani da su a yau da kullum.

Jaridar The Cable ta ce an samu hauhawar farashin kayayyaki daga 22.04 cikin dari zuwa 22.22 cikin dari a tsakanin watan Afrilu zuwa Mayun 2023.

NBS ta ce hauhawar da aka samu a watan Afrilu na da alaƙa da yadda aka yi ta samun hawan farashin a kowane wata tun daga farkon shekarar da muke ciki zuwa yanzu.

NBS ta ƙara da cewa kayayyaki irin su abinci, abubuwan sha, gidaje, ruwa, wutar lantarki, iskar gas, man fetur da sauran su ne suka ɗaga matsayin CPI din.

Biyo bayan wannan sanarwar ta NBS, wasu sun riƙa danganta hauhawar farashin kayayyakin da mulkin shekaru takwas na gwamnatin shugaba Buhari.

Sai dai, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Garba Shehu ya ce annobar cutar korona ce ta jawo koma bayan tattalin arzikin duniya kuma babu wata ƙasa da abun bai shafa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: