Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani ma’aikacin hukumar babban birnin tarayya Abuja tare da wasu akalla mutane 15 a rukunin gidaje 1,000 da ke Pegi a karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja.

Manema labarai sun ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe, sannan suka yi awon gaba da mutanen da suke komawa gida daga aiki.
Shugaban kungiyar mazauna garin Pegi Taiwo Aderibigbe ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Talata, inda

bindigar sun kai farmaki gidan ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe, sannan suka yi awon gaba da mutanen da suke komawa gida daga aiki.

Shugaban kungiyar mazauna garin Pegi Taiwo Aderibigbe ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Talata, inda
ya kara da cewa daga cikin wadanda aka sace har da ma’aikatan sashen kula da ci gaban babban birnin tarayya Abuja a karkashin hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja.
Aderibigbe ya ce, yan bindiga sun sace
mutane 15 a kan titin Pegi mai nisan kilomita 14, kuma daga cikin wadanda aka sace akwai Shu’aibu Musa, ma’aikacin FCTA.
Masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi iyalan wadanda suka sace ba a halin yanzu, amma jami’an tsaro na kokarin gano wasu mazauna garin da aka sace.
Kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ba ta amsa tambayoyi kan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, duk da kiran waya da sakon kar ta kwana da aka aike mata.