Mai alfarma sarkin Musulmi Allahji Sa’ad Abubakar Na III yayi kira ga ‘yan Najeriya akan a biye banbancin Addini da Siyasa bayan rantsar da sabuwar gwamnatin a ranar 29 ga watan Mayu.

Alhaji Sa’ad ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a gurin kaddamar da kwamitin babban Masallacin Kasa ANMMB tare da kwamitin amintattu kan manufofin ilmi Lafiya da kuma Jinkai MESH.
Sarkin ya bukaci ‘yan Najeriya da su ajiye dukkan wani banbancin addini siyasa Al’ada su hadu waje guda domin goyan bayan sabuwar gwamnati mai zuwa.

Kazalika ya bayyana cewa a halin da ake ciki a yanzu lokaci ne da kowanne dan Najeriya zai bayar da gudunmawarsa a milkin Demokradiyya wanda aka Fara tun a shekarar 1999.

Sannan ya roki ‘yan Najeriya da su bayar da hadin kai a yayin gudanar da bikin rantsuwa da za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.