Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa bayan karewar wa’adinsa zai yi kewar wasu mutane a zamanin Mulkin sa.

Mai magana da yawun shugaba Buhari na Musamman Femi Adesina ne ya tabbatar da hakan.


Shugaban ya bayyana cewa bayan ya bar kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu zai yi kewar mutanen kirkin da yayi aiki tare da su a gwamnatin sa.
Adesina ya ce sun yiwa shugaba Buhari tambayar ne shida ‘yan jaridar fadar Shugaban a birnin Landon, inda ya bayyana musu cewa zai yi kewar mutanen kirkin da yayi aiki tare da su tsawon shekaru Takwas ciki harda wadanda su ka yi masa tanbayar.
Adesina ya kara da cewa yayi wa shugaba Buhari aiki tukuru tare da sauke nauyin da aka dora masa.
Femi Adesina ya ce zai bar fadar shugaban Kasa a ranar Juma’a 26 ga watan Mayun da muke ciki a matsayin wanda aikin sa ya kare a fadar.