Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC ta tabbatar da cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ta ke zargi da aikata almundahana su na kokarin barin Najeriya kafin ranar karewar wa’adin Mulkin su.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da take mayar da martani ga gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle akan zargi da yake yiwa shugaban hukumar Abdul-Rashid Bawa da ya nemi cin hancin dala Miliyan Biyu a hannunsa.

EFCC ta ce matukar Matawalle da gaske yake ya gabatar da hujjoji akan zargin da ya ke yiwa Bawa.

Hukumar ta kara da cewa Gwamnan na Zamfara ya bijiro da zarge-zarge ne a lokacin da hukumar ta fara binciken sa kan sama da fadi da naira biliyan 70 na wasu ayyuka da aka bai’wa ‘yan kwangila amma ba su yi ba.

Gwamna Matawalle na daya daga cikin gwamnonin da za su bar Mulki a ranar 29 ga watan Mayu bayan ya sha kayi a hannun abokin takarar sa Dauda Lawal Dare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: