Aƙalla mutane 18 ne su ka rasa rayukansu yayin da aka kai hari ƙauyen Iye a jihar Benue.

An kai harin a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 07:00pm na yamma kusa da jami’ar Sarwuaan Tarka da ke Makurɗi babban binrin jihar.
Kauyen Iye na ƙarƙashin ƙaramar hukumar Guma a jihar Benue.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Catherine Anene ya tbbatar da faruwar hakan a safiyar yau Litinin.

Ya ce an gano gawarwaki gud bakwai yayin da aka hallaka guda cikin mutanen da su ka kai harin.
sai dai wani Christopher Waku mai bai wa shugaban ƙaramar hukumar Guma shawara a kan harkokin tsaro y ace mutane 18 aka hallaka a harin.
Hare-hare sun ci gaba da tsananta bayan kammala babban zaɓe a Najeriya wanda aka yi a watannin Fabrairu, Maris da kuma Afrilu.