Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta yi aiki tuƙuru wajen ganin ta buɗe jami’ar sufuri ta farko a garin Daura da ke jihar Katsina.

Ya bayyana cewa burin jami’ar shi ne samar da isassun ɗaliban da suka kammala karatun digiri, masu harkokin fasaha, ɓangaren sana’o’i, masu bincike a fannonin daban-daban na sufuri, musamman ma sufurin jiragen ƙasa.

Ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da ɗorewar ababen more rayuwa da gwamnatinsa ta zo da su kan harkokin sufurin jiragen na kasa.

Ya yi wannan jawabi ne a Legas, a yayin ƙaddamar da kamfanin Kajola na Jihar Ogun, wanda shi ne irinsa na farko a Afirka ta Yamma da zai riƙa samar da taragon jirgi 500 a duk shekara.

Buhari, wanda ministan sufuri, Muazu Sambo, ya wakilta ya ce saboda haka suna sa ran nan ba da jimawa ba ɗaliban da suka kammala karatu a Jami’ar Sufuri ta Daura, da waɗanda suka dawo daga jami’o’i daban-daban na kasar Sin waɗanda Messrs CCECC ta tura karatu, za su maye gurabensu a ma’aikatar Kajola

Leave a Reply

%d bloggers like this: