Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta sake kama fursononi biyu da ake zargin sun tsere a gidan gyaran hali na Kuje a Abuja suna aikata wani laifin.

Fursunoni da dama sun tsere daga gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin Abuja a watan Yuli na shekarar bara bayan ‘yan ta’adda sun yi amfani da abubuwan fashewa don fasa gidan gyaran halin.

Manema labarai sun ruwaito cewa akalla fursunoni 800 ne suka tsere daga gidan gyaran hali na Kuje a shekarar bara da ke dauke da fursunoni 994.

Mafi yawa daga cikin wadanda suka tsere din an kama su a wurare daban-daban na fadin kasar, wanda yayin kai harin ya yi sanadiyar mutuwar jami’in tsaro da kuma fursunoni guda hudu.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Suleiman Nguroje a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 22 ga watan Mayu, ya ce fursunonin biyu an kama su ne a kokarin da suke yi na satar shanu da sauran ayyuka munana.

Rundunar ta bayyana sunayensu da Atiku Ibrahim mai shekaru 37 da Adamu Ibrahim shi kuma mai shekaru 40 wadanda an dade ana nemansu ruwa a jallo tun bayan lokacin da aka fasa gidan gyaran halin.

bayyana sunayensu da Atiku Ibrahim mai shekaru 37 da Adamu Ibrahim shi kuma mai shekaru 40 wadanda an dade ana nemansu ruwa a jallo tun bayan lokacin da aka fasa gidan gyaran halin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Afolabi Babatola ya ba da umarnin a mika su ga jami’an gyaran hali na jihar Adamawa don daukar mataki na gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: