A cikin kwanakin da suka rage na shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa, ministoci sun fara miƙawa manyan sakatarorin dindindin na ma’aikatunsu kujerunsu gabanin rushe majalisar ministocin.

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu 2023, wa’adin mulkin shugaba Buhari na shekaru takwas, wanda ya fara daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa yau zai zo karshe.

Ministan ma’aikatar sadarwa da tattalin arziƙi, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya gudanar da aikinsa na kusa da ƙarshe a makon da ya gabata lokacin da ya kaddamar da wani kwamiti kan kuɗaɗen yanar gizo (blockchain) a Abuja.

Haka nan ma yau Laraba, ministan ya wakilci shugaban ƙasa wajen wani taron ci-gaban tattalin arziƙi da aka gudanar a ma’aikatar kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Fesbuk.

Kamar yadda wasu ministocin suka fara shirye-shiryen barin ofis, alamu na nuni da cewa shima ministan sadarwar ya fara haɗa kayansa don barin ofis.

Jaridar Daily Trust ta ce wani da ke aiki a ma’aikatar sadarwa ta ƙasa, ya bayyana cewa ya ga ma’aikatan ofishin ministan na kwashe takardu da wasu kayayyakinsa daga ofis a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

A nasa ɓangaren, ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Bello, ya bayar da umarnin rusa shaguna a babbar kasuwar UTC da ke Area 10, da kuma wasu gidaje a Gishiri da dai sauransu

Leave a Reply

%d bloggers like this: