Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta bayyana cewa akwai wasu mutane da ke shirin tayar da rikici a ranar rantsar da sabbin shugabannii a ranar 29 ga wata mayu.

A yau Alhamis 25 ga watan Mayu ne kakakin hukumar ta DSS Peter Afunanya ya bayyana haka a taron da yayi da yan jarida a helkwatar hukumar.
Ya ce sun samu bayanai akan cewa wasu daga cikin yan tayar da zaune tsaye za su kai hari lokacin da ake rantsar da sabbin shuwagabbanni.

Sai dai hukumar cikin bayannnata ta ce za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaron kasar don magance duk mai shiri na kai hari a lokacin.

Sannan hukumar ta bayyana cewa Yan jaridu kungiyoyi na fararen hula su tabbatar sun bi kaidojin aikin su a ranar domin kaucewa duk wata hayaniya.
Sannan hukumar ta shawarci jama a su daina yarda da kowannne irin zance da suka ji don hakan yana kara rura wutar lamarin.
Peter Afunanya ya ci gaba a cewa suna mai kira da mutane indai basu da wani katin shaida kada sun dinga shiga ko ina a lokacin rantsuwar.
A ranar 29 ne ake saran za a rantsar da sabbin shuwagabbani da aka zaba wadanda suka hada da gwamnoni da kuma yan majalisu sai shugaban kasa da mataimakinsa.
- Bayan gayyatar shuwagabannin kasashen Duniya.