Yau gareka!!!
Tsarabar shugaba mai jiran gado
Rubutawa
Abubakar Murtala Ibrahim
(Abban Matashiya)
abbakarmurtala1@gmail.com
+2348030840149
Shekaru takwas shugaban ƙasa ya shafe da wasu gwamnonin yayin da wasu gwamnonin su ka shafe shekaru huɗu a kan karagar muƙamai na zaɓe ko naɗi a mataki daban-daban, yau batu ake saura kwana biyar duniyar mulkin ta juya zuwa ga wasu.

Tuni shirye-shirye su ka yi nisa don karɓa da kuma miƙawa daga masu barin gado zuwa masu jiran gado bayan zaɓen da mutane su ka yi wanda demokaraɗiyyar Najeriya ta bai wa ƴan ƙasa dama.

Tabbas akwai babban darasi ga masu barin gado, da masu jiran gado da kuma talakawan da ake mulka.

Dukkan wani shugaba akwai nasa salon mukin da kuma yadda yake kallon lamuran yadda zai jagoranci al’ummarsa, hakan ya sa ya ke zaɓar mutane da za su dafa masa aikin mulkinsa don kai wa ga nasara a kan muradin da ya sa a gaba.

Babbar nasara ce ka kasance da masu faɗa maka gskiya a tare da kai kowanne lokaci, tare da kaucewa duk wani da zai zigaka don biyan buƙatar kansa.

Duniya juyi-juyi, akwai ƴan daɗi mulki da ya kan sa su sauya daga halayensu na ƙwarai, da kuma masu son fantamawa a kan yadda rayuwarsu ta kasance saboda matakin da su ke kai ko za su samu a gaba.

Waɗanda su ke kai ya zama izina a gareku.
Da ma shugabanci ya gaji haka, ko ka yi mai kyau ko akasinsa, dole wataran za a ambaci wani kai kuma a kiraka da tsoho.

Alkairinka shi zai ci gaba da binka tare da mutanen da za su kasance da kai ko bayan babu mulki ko muƙami.

Abu mafi sauƙi a rayuwar shi ne kallon wanda hakan ta kasance da shi a baya don kai ma a wannan layin kake.

Babu shakka duk abin da mutum ya mallaka na aro ne domin ita kanta duniyar ma an yi mata wa’adi da za ta ƙare, sannan idan ka ganka a mataki kada ka manta cewar wani ne ya bar wajen kafin ka tsinci kanka a wajen. Adalcin da za ka yi wa kanka domin samun sauƙin rayuwa shi ne ka fara lissafa kanka a matsain wanda zai shuɗe tun daga ranar da ka samu damar damawa.

Tabbas kowanne shugaba ko jagora akwai alkhairinsa da jama’a za su gani idan baya nan, haka zalika abin da ya shuka akasin alkhairin, shi zai fi ganinsa a zahiri bayan dama ta kufce masa.

Kamar yadda wasu masu hikima ke faɗa cewar, wasu shugabannin ko masu dama ana sauya musu kansu ya koma na wata halitta, yayin da damar ta ƙare sai a dawo musu da ainihin kawunansu a nan fa za su gane irin kuskuren da su ka aikata wanda babu damar gyarawa tunda wa’adi ya ƙare.

Wasu kuwa na mafani da damarsu wajen gina na ƙasa da kuma barin kyakkyawan tarihi wanda ko ba sa raye ba za a manta da su ba, sannan za a dinga bibiyar zuriyar da su ka bari.
Da yawa na samun dama su manta da waɗanda su ke tare ko su ka taimakesu a baya, wanda hakan ke zama babban kuskure domin damar na zuwa ne ta wani lokaci ta ƙare, kuma yayin da ta ƙare babu wani abu da ya yi saura sai rayuwa da mutanen da aka taso tun asali.

Akwai ƙalilan ƴan baiwa da ba a fatan su rasa damarsu ganin yadda mutane ke amfana da su da kuma yadda su ke ƙoƙarin sauke nauyin da ke wuyansu, Allah ya yi haka ne domin ajiye aya ga masu niyya daban-daban a rayuwa.

Babu shakka za a yi kewar wasu shugabannin a wasu matakan da su ka taka rawa, kamar yadda za a yi farin ciki da wasu da barin madafun da su ke kai.

Babban ƙalubalen da shugabanni a jihar Kano da Najeriya za su fuskanta bai wuce yadda mutane ke kallon kuskuren shugabanni masu barin gado ba zuwa kyakkyawan tunanin samun sauyi daga masu jiran gado.

Daga ciki akwai tsada da tsanani na rayuwa.
Talaka a har kullum burinsa bai wuce na abinda zai ci ya sha sannan a tsare masa rayuwa, lafiya da dukiyarsa ba, wannan kaɗai shugaba idan ya yi, ya sauƙaƙa mafi yawa daga cikin burinsa.

Yanzu siyasa ta ƙare, abinda ya rage shi ne shugabanci, ko dai ka shirya shugabantar al’umma don ai maka jiniya da raba muƙamai, ko kuma ka shirya shugabantar al’umma don saka musu a kan buƙatun da su ka aike maka.
Shawara!
Tun da dai akwai mutane da su ke da basira da kuma ƙoƙarin kawo ci gaba wajen shugabanci, a ajiye a adawa a gefe a gayyato mutanen da su ke da son cigaban jama’a don amfanar da su.
Bayar da dama a gurbin da ya dace tare da ɗora nauyi ga wanda zai iya saukewa hakan zai taimaka wajen kawo cigaba, amma muddin aka kalli wahala ko hidima da wani ya yi tare da ɗora shi ko ba shi dama a wajen da bai cancanta ba don kawai ya taimaka wajen samun mulki, to tabbas za a yi tafiyar biri a yashi domin hakan ba zai amfanar da komai ba illa koma baya a matakin ƙasa ko jiha.

Zaɓi ya rge gareka (shugaba) domin yau ake ƙoƙarin ba ka mulki, ko da ka zarce a gaba ka tuna wata rana irin wannan ranar za ta zo gareka domin ka miƙawa wani.

Fatanmu har kullum Allah ya sa mu amfani damar da ya ara mana don kaucewa da na sani a ranar da wa’adi ya ƙare.

Abubakar Murtala Ibrahim
(Abban Matashiya)
abbakarmurtala1@gmail.com
+2348030840149
4 Zulƙida 1444
24/5/2023

Leave a Reply

%d bloggers like this: