Gwamnatin tarayyar Najeriya ta mayar da martani game da sukar da ake yi mata akan shugaba Buhari na ci gaba da bayar da kwangiloli a yayin da wa’adin mulkin sa ke daf da karewa.

Jaridar Vanguard a yau Juma’a ta rawaito cewa Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ya bayyana cewa sai daren da za su mika mulki ga sabuwar gwamnati za su daina aiki.
Ministan ya ce har tsakiyar daren ranar 29 ga watan Mayu gwamnatin shugaba Buhari za ta bayar da kwangiloli ko kuma ta karbo Bashi kudade.

Babatunde na wannan jawabin ne a gurin kaddamar da fara aikin fadada titin Akure zuwa Ado Ekiti a garin Akure na Jihar Ondo.

Titin mai kilomita 49 zai lashe naira biliyan 90,inda za a kara girman hanyar akan a kara gyrata.
Tunde ya bayyana cewa kamfanonin Kopeck Construntion da Samchase Nqjeria Ltd ne za su gudanar da aikin fadada titin kuma za a kammala nan da shekaru biyu masu zuwa.