Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar gabatan akan kalubalantar nasarar da Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima su ka samu a zaben da aka gudanar.

Kotun mai alkalai biyar ta ya watsi da karar ne a yau Juma’a bayan zaman kotun ta ce jam’iyyar ta PDP ba ta da hurumin shigar da kara tunda ba mambar jam’iyyar APC bace.
Masu shigar da karar sun bayyana cewa zaben Kasim Shettima a matsayin mataimaki Tinubu ya sabawa sashi na 29 (1) da sashi na 33 da 35 da sasahi 84(1) (2) na dokar zabe a Najeriya a shekarar 2022 da ta gabata.

Masu karar sun kara da cewa mataimakin shugaban Kasar Kashim Shettima ya sabawa doka sakamakon tsayawa takarar mataimakin shugaban Kasa tare kuma da neman kujerar majalisar Dattawa ta Borno ta tsakiya a lokaci guda.

Akan hakan wadanda su ka shigar da karar su ke neman kotun ta soke ingancin jam’iyyar ta APC da Tinubu da Shettima daga takarar da su ka tsaya na shugaba da Mataimaki.