Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta samu nasarar kama wani magidanci mai shekaru 28 da ya yiwa ‘yarsa mai shekaru biyar Fyarde a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar Abimbola Oyeyimi ne ya tabbatar da kama mutumin bayan mahaifiyar yarinya ta shigar da kara Ofishin ‘yan sandan Jihar.
Abimbola ya ce mahaifiyar ta kai karar mijin nata ne bayan da ta lura yarinyar tana jin zafi a lokacin da ta tashi yin fitsari wanda hakan ya sanya ta titsiye yarinyar harta kai ga ta bayyana mata mahaifinta ne yayi lalata da ita.

Kakakin ya kara cewa bayan samun korafi da su ka yi daga mahaifiyar yarinyar hakan ya sanya Sula tura jami’an su domin hawowa da mijin matar.

Oyeyemi ya ce bayan kama mutumin da su ka yi a ranar 22 ga watan Mayun da muke ciki bai musanta zargin da ake yi masa ba.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Olanrewaju Oladimeji ya bayar da umarnin aikewa da shi sashin binciken manyan laifuka na CID domin gudanar da bincike akan sa.