Gwamnan Jihar Rivers mai barin gado Nyesom Wike ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnatin tarayyar Najeriya ta kara yawan kudaden da ta ke bai’wa rundunar ‘yan sanda.

Haka na kunshe ta cikin wata sanarwa da Sakataren gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook mai dauke da sa sannun mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan shafukan sada zumunta Kelvin Ebiri.

Gwamnan Wike ya yi wannan Jawabin ne a wajen ƙaddamar da cibiyar fasaha ta hukumar ‘yan sanda a karamar hukumar Obio/Akpor.

Wike ya kara da cewa gwamnatinsa ta fahimci tasirin samar da kayan aiki wanda hakan ya sanya ta ke kokarin samar wa da rundunar ‘yan sandan Jihar wadatattun kayan aiki.

Gwamnan y ace hakan zai bai wa hukumar ta ‘yan sanda damar sauke nauyin da aka dora mata.

Wike ya kara da cewa dukkannin gwamnatin da ba za ta iya kare rayuka da dukiyoyin al’umma da dakile muyagun dabi’u ba, to ba ta da wani alfanu ga Al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: