Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutun ma’aikata sakamakon bikin rantsar da sabuwar gwamnatin Najeriya.

Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.


Jaridar Nation ta rawaito cewa gwamnatin ta dauki matakin hakan ne domin murnar rantsar da sabuwar gwamnati ta 16 da za a gudanar a ranar Litinin.
Aregbesola ya mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya ga wanna rana mai dumbun tarihi ga ‘yan Kasa.
A wata sanarwa da Sakataren Ma’aikatar cikin gida Dakta Shu’aibu Belgore ya fitar ministan ya roki ‘yan Najeriya su ci gaba da goyon bayan bunkasa demokradiyya ta hanyar bin doka da Oda.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su hadu guri guda wajen goyon bayan sabuwar gwamnatin da za a rantsar domin hadin kan mutane shine tushen Najeriya.