Wata kungiyar siyasa ta Ahlulbayt Political Forum da ke karkashin kungiya mai akidar mabiya Shi’a IMN reshen Jihar Kaduna ta nuna rashin jin dadinta akan yadda gwamnatin Jihar Kaduna ke ci gaba da aikin rushe wurare a Jihar akan ‘yan kungiyar da sauran mutane.

 

Sakataren kungiyar Suleiman Muhammad ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Juma’a.

 

Ya ce kungiyar su ta shiga sahun sauran kungiyoyin Jihar masu zaman kansu akan nuna rashin jindadin su dangane da rusan da ake yi a Jihar.

 

Kungiyar ta ce hakan zai iya kawo tabar-barewar zaman lafiyar da Jihar ke samu.

 

Suleiman ya kara da cewa suna mai kira ga gwamnati da ta martaba rayuka da dukiyoyin Al’ummar ta kamar yadda kundin tsarin mulkin Kasa ya tanada.

 

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati mai jiran gado da ta Samar da hanyoyin magance yawaitar rikicin da ake fama dashi a Jihar.

 

Sannan yayi kira ga wadanda abin ya Shafa da su gujewa daukar doka a hannu su nemi hakkin su ta bangaren doka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: