Zababben gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya aike da sakon gayyata ga tsohon Sarkin Kano Muhammad Sunusi Na II gurin bikin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

 

Hakan na kunshe ne ta cikin wata takarda da zababban gwamnan ya sanyawa hannu mai duke da kwanan watan 26 ga watan Mayu.

 

Takardar ta bayyana cewa halartar Sunusi gurin bikin rantsuwar hakan zai kara musu goyon bayan da su ke dashi a gurin Al’umma.

 

Wani daga cikin kwamitin karbar mulkin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun yanke shawarar gayyatar manyan mutane zuwa wajen bikin rantsar da zaɓaɓɓen gwamnan.

 

Shi ma wani makusanci ga tsohon Sarkin ya bayyana cewa Sarki Sunusi bai bayyana cewa zai je ko ba zai je ba, sakamakon gayyatar shi da aka yi guraren rantsuwa har guda biyu da na shugaban Kasa da kuma na gwamnan Jihar Abia.

 

Sannan ya ce Tsohon sarkin ya bar gida Najeriya a ranar Juma’a zuwa Kasar Afirika ta Kudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: