Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusif ya karɓi rantsuwar fara aiki a yau Litinin.

Abba Kabir da mataimakinsa Aminu Abdussalam a filin taro na Marigayi Sani Abacha da ke unguwar ƙofar Mata a Kano.

Daga cikin jawabin sabon gwamnan Kano, y ace zai mayar da hankali wajen gina ayyuka tare da ɗorawa a kan aikin tsohon gwamna Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Sannan ya ce za su tabbata sun farfaɗo da ayyukan da gwamnatin da ta shuɗe ta baritare da inganta ilimi har ma da bayar da shi kyauta.

Haka kuma gwamnan y ace gwamnatin sa za ta ci gaba da aurar da zawarawa da kuma tsaftace jihar Kano tare da kawo ƙarshen daba da shan ƙwaya a jihar.

Idan ba a manta ba tsohuwar gwamnatin Kano ta yi dokar ayyana fashin waya.

Dubban mutane ne su ka halarci taron ciki har da sarakunan Kano.

Kafin rantsar da sabon gwamnan, an miƙa kundin bayanai a kan mulkin Kano daga tsohuwar gwamnati wanda ake bi bashin sama da biliyan 200.

Sai dai gwamna Abba abir Yusif ya ce gwamnatinsa za ta bibiya a kan bashin da gwamnatinsa ta gada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: