Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce daga yanzu ya soke biyan tallafin man fetur a Najeriya.

Bola Tinubu ya ce bayar da tallafin man fetur da kasar ke yi ya na taimakon masu arzikin kasar ne kadi ba talakawan kasar ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a yayin jawabinsa da ya yi a yau bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya na 16.

Daga cikin jawabinsa, Bola Tinubu y ace zai bai wa ɓangaren noma muhimmanci domin samar da hanoyiyin bunkasa kayan amfani nay au da kullum.

Ya ce ya na fata hakan zai taimaka wajen rage tsadar kayan abinci da ake fama da shi a kasar wanda y ace zaa a tallafawa manoma domin ganin burin ya cika.

Haka kuma Bola Tinubu y ace zai duba batun sauya fasalin kuɗi da tsohuwar gwmnatin shugaba Buhari ta aiwatar a baya.

Sannan y ace gwamnatinsa za ta tabbata ta tsare kauyukan ƙasar domin rage asarar da ake yin a dabbobi da sauran kayayyaki.

Bola Tinubu ya sha rantsuwar fara aiki a yau a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: