Tsohon mai bai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, shawara na musamman kan yaɗa labarai, Femi Adesina, ya samu aiki kwanaki kaɗan bayan sauka daga mulki.

Manema labarai sun ruwaito cewa tsohon kakakin Buhari zai fara aiki a matsayin mataimakin shugaban kamfanin jaridar The Sun daga ranar 1 ga watan Satumba, 2023.

Adesina ya rike muƙamain shugaban marubutan jaridar The Sun kafin daga bisani tsohon shugaban ƙasa Buhari ya naɗa shi a matsayin mai magana da yawunsa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Mista Adesina ne da kansa ya tabbatar da samun wannan aiki a wata hira da ya yi ranar Talata.

A cewar Adesina, bayan Buhari ya naɗa shi mukami, ya yi niyyar murabus daga aikin jaridar TheSun, amma Sanata Kalu ya ba shi shawarar kar ya yi kuskuren yin murabus.

Ya ce a wannan lokaci Kalu ya masa tayin dawowa kan aiki idan muƙamin gwamnatin bai masa ba ko kuma bayan sun gama mulki na tsawon shekaru Takawas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: