Dole Ne Jami’an Tsaro Su Ƙara Ƙaimi A Kan Aikinsu – Tinubu

 

Shugaban kasar Najeriya Ahmed Bola Tinubu ya ja hankali ga manyan jami’an tsaro ƙasar da su kara himma da dagewa don Samun tabbataccen zaman lafiya a kasar.

 

Shugaban ya sanar da hakanne yayin ganawarsa da shugabanin hukomomin tsaron kasar karo na farko a fadarsa da ke Abuja.

 

Yayin ganawarsa da manaima labarai bayan kammala zaman mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro yace shugaban sam ba zai lamunci yanayin da kasar take ciki ba.

 

Bola Tinubu ya ce bai dace kasar ta kara zama koma baya ba lokacin da sauran kasashen duniya ke ci gaba.

 

Ya kara da cewa wajibi ne a samu hadin kai tsakanin dukkanin sauran bangarorin tsaro ta fuskar tsaro.

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: