Majalissar dattijan Najeriya ta bayyana cewa za a gudanar da bincike akan wasu kudade da aka kashe don gyara matatun tace man fetur a kasar Najeriya.

 

Kamar yadda majalissar ta bayyana ta ce dole a yi bincike akan wadannan kudaden da aka hallaka kimanin Dala Biliyan 10 cikin shekaru Goma ana gyaran matatar.

 

Sannan ta ce bayan kashe wadannan kudin, matatun guda hudu ba sa yin aiki kaso 30 cikin 100.

 

Fadin hakan ya biyo bayan furcin shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu na cire tallafin man fetur da yayi a ranar Litinin 29 ga wata biyar.

 

Sannan ake ci gaba da samun cinkoso a gidajen mai.

 

An bayyana cewa kasa Najeriya ita ce kasar da tafi kowacce kasa a fadin kasashen Afrika arzikin man fetur.

 

Inda kuma take siyar da danyen manta a kasuwar Duniya sannan ta siyo tacecce da tsada.

 

Amma dai a watan gobe ne ake sa ran babbar matatar mai ta DanGote za ta fara aikin tace man.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: