Hukumar kiyaye hadurraya kasa FRSC ta ba bayyana cewa mutane takwas ne suka rasu bayan da wani hatsari ya auku a jihar Bauchi.

Kamar yadda hukumar ta kiyaye hadurra ta bayyana ta ce hatsarin ya faru ne akan babbar hanyar Darazo zuwa Bauchi ajiya Laraba 31 ga watan mayu.


Ta ce hatsarin ya faru da misalin karfe 1:43 na rana inda bayan haduwar motar kirar Hilux da kuma wata motar daukar fasinja Golf.
Sannan hatsarin ya rutsa da mutane 14 mata bakwai maza bakwai inda maza hudu suka rasu da mata hudu ciki harda yara kanana.
Sannan akwai wadanda suka Samu raunuka a jiki.
Sai dai kamar yadda hukumar ta kiyaye hadurra ta bayyana ta ce ta mika sauran masu rauni izuwa asibitin Darazo.
A ko da yaushe hukumar kiyaye hadurran ta na bayyana cewa direbobi su guji gudun wuce kima duba da yanayin damina ne a yanzu.